XtGem Forum catalog
HomeBlogBARKA DA ZUWA DANDALIN DAMAGARWA ZINDER TA JANHURIYAR NIGER. FILINE: NA FADARKAWA NISHADANTARWA DA ILMANTARWA HARDA SADA ZUMUNCI.Zinder garin mune
Tags: FADARWAR

SAKO ZUWA GA MATASSA

WASIKA ZUWA GA MATASA MASU AIKATA ISTIMNA'I ISTIMNA'I = fitar da mani ko sha'awa da gangan ta hanyar da bata dace ba. Matasa Maza da mata, suna neman taimako akan illolin da suke samu ajikkunansu sakamakon Istimna'i wato Masturbation. an kawo hujjoji gamsassu daga Alqur'ani da Sunnar Ma'aikin Allah (saw) da fatawoyin Amintattun Malamai duk akan HARAMCIN ISTIMNA'I. Amma duk da haka wasu matasan basu yarda sun dena ba. Wasu kuwa sunji tsoron ALLAH sun riga sun dena. Babban dalilin da yake janyo musu afkawa cikin wannan bala'in shine : 1. Kallon Fina-finan batsa. 2. Shiga shafukan internet na batsa. 3. Yin zantukan batsa tsakanin saurayi da budurwa. 4. Kusantar zina ta hanyar kallo da shafa, ko zance da dai sauransu. Wasu kuma suna aikata hakan ne don gudun afkawa ZINA, basu san cewa shi dinma ZINAR bane!! Idan kun Qi bari domin Allah, to ku dubi irin illolin da yake haifar muku ajikinku mana!!! 1. MUTUWAR IDANU. 2. MUTUWAR AL'AURA. 3. CIWON BAYA. 4. BUGAWAR QIRJI. 5. RIKICEWAR TUNANI. 6. YAWAN MANTUWA. 7. KARANCIN 'YA'YAN MANIYYI. 8. SAURIN INZALI. 9. SHAFAR ALJANU, ETC. Wadannan 'yan kadan ne daga cikin Matsalolin da ISTIMNA'I yake haifarwa. kuma duk wanda bai tuba ya dena ba, idan ya mutu ahaka zai je ya tarar da hisabi. DON GIRMAN ALLAH!! Matasa ku kiyayi zina da duk dangoginta. ku kaurace ma duk wani abinda zai rika motsa muku sha'awa. Idan da hali kuje kuyi aure. idan kuma babu hali, to ku yawaita azumi. ALLAH YA SAWWAKE. Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA, DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM, WHATSAPP, da sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana. Manzon Allah (saww) yace: "WALLAHI IDAN ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA, YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA" Wani mutum yazo wajen manzon Allah S. A.W. ya ce: . Yah-manzon-rahma zan tambaye ka rayuwar duniya da ta lahira. . 1, Yah-manzon Allah ina son in zama mafi sani a cikin mutane? AMSA,, sai ya ce "Ka ji tsoron Allah ka bi dokokin Sa." . 2, Ina son na zama mafi arziki a cikin mutane? . AMSA,, sai ya ce "Ka zama mai wadatar zuci." . 3, Ina son na zama Wanda yafi kowa acikin mutane? AMSA,, sai ya ce "Ka zama mai amfanarwa." . 4, Menene zai kare ni daga wuta? AMSA,, sai ya ce "Ka zama mai yawan yin Azumi." . 5, Ina son na zama mafi adalci a cikin mutane? . AMSA,, sai ya ce "Ka so ma dan'uwan ka abin da ka ke so ma kan ka." . 6, Ina son na zama mafi amfanin mutane a wajen Allah? AMSA,, sai ya ce "Ka yawaita tuna Allah." . 7, Ina son imanina ya zama ingantacce? AMSA,, sai ya ce "Ka gyara halayen ka." . 8, Menene yake huce fushin Allah S. W .T.? AMSA,, sai ya ce "Ba da zakka a boye da kyautata wa ya'n uwa." . 9, wani zunubi yafi muni awajen Allah? AMSA,, sai ya ce "Mummunar hali shine rowa" . 10, Ina son na zama mafi biyayya ga Allah? AMSA,, sai ya ce "Ka bi umurnin Allah za ka zama mafi rinjaye a wurin Allah." . YA ALLAH Ka sa mu gama da Duniya lafiya ameeeen
Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE
ZINDER GARIN MALAMMAI
Please log in or sign up to chat
ZINDER GARIN MUNE
Mobile Search : http://zinderniger.wapdale.com/sea rch/index.php?site= howi.in SMS IN : http://zinderniger.wapdale.com/sms /index.php?site=howi. in Image Mastero http://zinderniger.wapdale.com/ima ge/index.php?site= howi.in Facebook Share : http://zinderniger.wapdale.com/fac ebook.php?site=howi. in&status=howi.in Live Calculator : http://zinderniger.wapdale.com/gam es/lovecalculator.php ?site=howi.in