XtGem Forum catalog
HomeBlogBARKA DA ZUWA DANDALIN DAMAGARWA ZINDER TA JANHURIYAR NIGER. FILINE: NA FADARKAWA NISHADANTARWA DA ILMANTARWA HARDA SADA ZUMUNCI.Zinder garin mune

AIYUKA MASU SAUKIN SA MUTUN A ALJANA

AIYUKA MASU SAUKIN SA MUTUN A ALJANA
»» DAGA CIKIN AIYUKA MASU SAUKI DA SUKE KAI MUTUM ALJANNA «« 1- Kulawa da Maraya: Annabi (S.A.W.) yace: (Ni da mai daukar nauyin Maraya a aljanna kamar haka muke, sai yayi nuni zuwa ga yatsarsa manuniya da ta tsakiya sai ya buda tsakaninsu). @ ﻩﺍﻭﺭ 2 . ﻱﺭﺎﺨﺒﻟﺍ- Yin Zikiri bayan gama alwala: Manzon Allah (S.A.W.) yace: (Babu wani daga cikin ku da zaiyi alwala sannan ya kyautata alwalarsa, sannan bayan ya gama yace: { ﻚﻳﺮﺷﻻ ﻩﺪﺣﻭ ﻪﻠﻟﺍ ﻻﺇ ﻪﻟﺇﻻ ﻥﺍ ﺪﻬﺷﺍ ﻪﻟ ﻮﺳﺭﻭ ﻩﺪﺒﻋ ﺪﻤﺤﻣ ﺎﻧﺍ ﺪﻬﺷﺍﻭ ﻪﻟ }. face an bude masa kokofin aljanna guda Takwas, yana shiga ta inda yaga dama). @ 3 . ﻢﻠﺴﻣ ﻩﺍﻭﺭ- Yin Sallar Assuba da La'asar acikin Jam'i: Annabi (S.A.W.) yace: (Duk wanda ya sallaci Sanyi guda biyu, “yana nufin sallar assubà da La'asar” ya shiga aljanna). @4 . ﻢﻠﺴﻣﻭﻱﺭﺎﺨﺒﻟﺍ- Kiyaye Salloli guda biyar na Farillah akan lokacinsu: Annabi (S.A.W.) yace: (Dukkan wanda ya sallaci sallolin farilla akan lokacinsu, yana da alkawali awajan Allah ya shigar da shi Aljanna) @ ﻲﺋﺎﺴﻨﻟﺍﻭ . ﺩﻭﺍﺩ ﻮﺑﺍﻭ ﺪﻤﺣﺍ ﻩﺍﻭﺭ 5 .- Yin biyayya da kyautatama iyaye: Manzon Allah (S.A.W.) yace: (Allah ya tumurmusa hancinsa, Allah ya tumurmusa hancinsa, Allah ya tumurmusa hancinsa, sai akace wanene ya Manzon Allah?? sai yace: Wanda ya riski mahaifansa guda biyu ko guda daya bayan girma ya kamasu, sannan bai shiga Aljanna ba. @ 6 . ﻢﻠﺴﻣ ﻩﺍﻭﺭ- Kiyaye Harshe da al'aura: Annabi (S.A.W.) yace: (Wa zai kiyaye min tsakanin labbansa guda biyu “yana nufin harshe" da al'aurarsa, ni kuma zan lamince masa shiga aljanna) @ ﻩﺍﻭﺭ 7 . ﻱﺭﺎﺨﺒﻟﺍ- Yin Sallah raka'a biyu bayan alwala, tare da halarto da zuciya lokacin sallar: Annabi (S.A.W.) yace: (Babu wani musulmi da zaiyi alwala sannan ya kyautata alwalarsa, sannan yayi sallah raka'a biyu, ya fuskanci Allah acikin sallarsa da zuciyarsa da fuskarsa, face Allah ya bashi aljanna). @ ﻢﻠﺴﻣ ﻩﺍﻭﺭ . Ya Allah ka bamu ikon aikata ayyukan da zaka yarda damu saboda su. »»»»» AMEEN «««««
Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE
ZINDER GARIN MALAMMAI
Please log in or sign up to chat
ZINDER GARIN MUNE
Mobile Search : http://zinderniger.wapdale.com/sea rch/index.php?site= howi.in SMS IN : http://zinderniger.wapdale.com/sms /index.php?site=howi. in Image Mastero http://zinderniger.wapdale.com/ima ge/index.php?site= howi.in Facebook Share : http://zinderniger.wapdale.com/fac ebook.php?site=howi. in&status=howi.in Live Calculator : http://zinderniger.wapdale.com/gam es/lovecalculator.php ?site=howi.in