TARIHIN DAULAR BORNO
Daular Borno tsohuwar Daula ce a
Afirka da aka kafa tun kafin karni
na 10 wacce ta hada da yankunan
da yanzu ke cikin Najeriya da Nijar
da Chadi da Kamaru da Sudan har
Libya. Daular Kanem ta El Kanemi ta samo
asali ne daga daular Saifuwa. Masana tarihi sun ce mutanen Saifuwa
daga Yemen ne suka fara kafa daular
musulunci a Borno, tsawon shekaru
1000 da suka gabata. Muhammad al-Amin ElKanemi ya kafa
Daular Kanem ne a karni na 18, bayan
kawar da daular Saifuwa wadanda
sarakunanta suka yi mulki shekaru
da dama. BBC Hausa ta duba tarihin Daular
Borno ta hanyar tattaunawa da
Masana tarihi Alhaji Zanna Hassan
Boguma daraktan da ke kula da
al'amuran masarautu a Borno, da
Farfesa Adam Muhammad Ajiri na sashen nazarin addinin Islama a
Jami'ar Maiduguri, wadanda kuma
suka yi kokarin amsa wasu
tambayoyi da masu saurare suka
aiko. Asalin kalmar Borno - Tambaya ce da muka samu daga Umar Abubakar da Sani Garba da Ishaq Abubakar Kazaure. Rubuce-rubucen masana tarihi sun
nuna cewa Kalmar Borno ta samo
asali ne daga kalmomin Larabci,
"Bahar Nur" wato ma'ana kogin
haske. Kuma saboda kasancewar Borno
gidan Al Qur'ani gidan Musulunci ne
dalilin ke nan da ya sa sarakunan
farko suke kiranta "Bahar Nur",
ma'ana kogin haske na musulunci. Amsar tambayoyinku kan masarautar Sarkin Musulmin Nigeria Mata 100: Kun san macen da ta yi zarra tsakanin mazan Nigeria? Masanin tarihi Alhaji Zanna Hassan
Boguma ya ce Ibn khaldun ya ambaci
"Bahar Nur" a rubuce-rubucensa na
tarihin musulunci a Afirka. Tushen Borno - Wannan Tambaya ce da muka samu daga Umar Musa Dambam daga Bauchi a Najeriya da Buhari Yusuf da Abdulmumin Adamu da Ahmad Adamu Tamadina da Shu'aibu Idris Kofar fada Balangu a jihar Jigawa da Garba Saleh. Tarihi ya nuna cewa Kanuri da suka
kafa Borno daga Yemen suka fito,
wato tsatson wani sarki da aka yi a
Yemen Said Ibn Dhi Yazan da ake kira
Malik al-Himyari tun kafin zamanin
Annabi SAW, wanda ya kafa dauloli a India da Fasha. Tarihi ya nuna mutanen Ibn Dhi Yazan
suna cikin wadanda suka amince su
ba sahabban Annabi SAW mafaka
bayan hijirarsa daga Makkah zuwa
Madinah. Yemen ne asalin Kanurin da suka kafa
mulki a Borno daga daular Saifuwa' a
cewar Zanna Hassan Boguma. Borno a zamanin Sahabbai - Tambaya ce da muka samu daga Jamilu Bagaraje da Magaji Rabiu da Abubakar Umar Usman da Nasir Abubakar Jaja. Daular Borno ta yi zamani da
Sahabbai, kuma masanin tarihi Alhaji
Zanna Hassan Boguma ya ce daular ta
kafu ne tun kafin zuwan Annabi SAW. A cewarsa tarihi ya nuna sarakunan
Borno sun aika da wasika suna
neman malamai da za su koyar da
addini zuwa ga Amr al-As gwamnan
Misra, wanda shi kuma ya tura Uqba
Ibn Nafi. "Sarakunan Borno sun karbi malamai
daga wajen Ibn Nafi a zamanin
Sayyadina Umar RA". Amma Zanna Hassan Boguma ya ce
wasu litattafan tarihi sun nuna cewa a
zamanin Sayyadina Usman RA ne. Sai dai Farfesa Adam Muhammad Ajiri
ya ce Gwamnan daular Maghribi a
arewacin Afirka Uqba Ibn Nafi
yakinsa har ya kawo Borno a
shekarar 666, kuma zamanin
Khulafa'ur Rashidun ya fara ne daga 632 har zuwa 660. Ya ce ba za a iya cewa sun yi zamani
da sahabbai ba, amma ana ganin
watakila a lokacin akwai daular
musulunci a Borno, ko da yake an fi
tabbatarwa a zamanin Umayyad daga
661 zuwa 750. "A lokacin akwai binciken da ya nuna
daga shekarar 661 zuwa 670 akwai
malamai daga daular Umayyad da
suka shigo yankin Maghrib har suka
iso Borno," in ji Farfesa Ajiri. Saifuwa a Borno da kafuwar ElKanemi - Tambaya ce da muka samu daga Abdurahman Salisu Zaria da Abubakar Goni Kolo da Hassan Yarima K/Huguma da Baba Ali Kabir Saifuwa su ne asalin sarautar Borno,
kuma Zanna Boguma ya ce dalilin da
ya sa ake kiransu Saifuwa saboda sun
fito ne daga Said Ibn Dhi Yazan. Tarihi ya nuna Saifuwa sun yi sarauta
sama da shekara 1000 inda suka yi
sarakuna kimanin 113, tun kafin
karni na bakwai. Farfesa Ajiri ya ce bayan Saifuwa sun
ci Zaghawa da yaki ne suka kafa
daular musulunci a Borno, kuma sun
kafa daula ne daga wajajen karni na
shida. Sarakunan farko a daular Saifuwa sun
hada da Mai Dugu a shekarar 785 da
Mai Fune a shekarar 835 da Mai Aritso
a 893, da Mai Katuri a 942 da Mai
Ayoma a 961 da Mai Bulu a 1019 da
Mai Arki a 1035 da Mai Shu a 1077. "Tun zamanin Sarkin Saifuwa Mai
Hume Djilme a wajajen 1080 aka fara
daula ta musulunci har zuwa sauran
sarakunan da aka yi", a cewar Zanna
Boguma. Ya ce, a zamanin daular musulunci ta
Saifuwa an yi Sarakuna da suka hada
da Mai Dunama Humemi da ya yi mulki
daga shekarar 1098 zuwa 1150 da
Mai Biri Ibn Dunoma da ya yi mulki
daga shekarar 1150 zuwa 1176 da Mai Bikoru Ibn Biri Dunomami da ya yi
zamani daga 1176 zuwa 1193. Mai Ahmad ne Sarkin Saifuwa na
karshe, kafin zamanin daular
ElKanemi. Farfesa Ajiri ya ce karshen mulkin
Saifuwa ya zo karshe ne a lokacin da
Fulani suka kawo hari suka ci garin
Gazargamu da yaki tsohon babban
birnin Daular Borno. Goni Mukhtar ne ya yaki Gazargamu,
inda ya kori Mai na Saifuwa tare da
taimakon Shehu El Kanemi. ElKanemi ne ya taimaka aka kori
Fulani daga Borno. Farfesa Ajiri ya ce bayan an kashe
Goni Muktar a Damaturu ne kuma Mai
Ahmad na Saifuwa ya rasu, daga nan
El Kanemi ya zama Sarki a wajajen
1810 zuwa 1814. ElKanemi ya ci gaba da mulki a daular
Saifuwa duk da cewa shi ba daga
zuriyar Saifuwa ba ne. Farfesa ya ce ElKanemi ya kafa daular
ElKanemi 1814 a birnin Kukawa, wato
shekaru sama da 200 a yanzu. "Idan an hada shekaru kusan 800 na
Daular Saifuwa da shekaru sama da
200 zai kasance shekarun daular
Borno sama da 1000". Shehu Mohammed el Amin Elkanemi
ya fara kafa daula ne a Ngurno tare
da ba Mai Dunoma na Tara Lefami
matsayin sarki a Kanem daga daular
Saifuwa daga 1814 zuwa 1817. Mai Ibrahim na hudu Ibn Dunoma
Lefami ne ya gaji Dunoma a matsayin
Sarkin Saifuwa a Kanem. Bayan El Kanemi ya karbi mulki ne
sarautar Borno ta sauya daga Saifuwa
zuwa Shehu ElKanemi. Masanin tarihi Zanna Boguma ya ce
lakabin sarautar Borno ya sauya daga
"Mai" ma'ana "Sarki" zuwa "Shehu"
bayan kafuwar ElKanemi, sabanin
sarakunan farko. "Bayan ElKanemi ya samu mulkin
Borno, daga nan ne ya ce shi ba zai
amince a kira shi da "Mai" ba saboda
shi malami ne". "Don haka ya ce zai kira kansa a
matsayin Shehu, wato Malami, inda ya
hada mulki da malamanta", a cewar
Zanna Boguma. Ya kuma ce: "Wannan ne dalilin da ya
sa duk wadanda suka zama sarakuna
a Borno ake kiransu Shehu daga
gidan El Kanemi." Shehu Umar Kura ne ya gaji
mahaifinsa Shehu Muhammad El Amin
ElKanemi a matsayin Sarkin Borno
daga 1835 zuwa 1853. Sarakunan El Kanemi - Tambaya ce da muka samu daga Naziri Aliyu Abubakar da Hussaini Aminu da Mohammed Mala Ngarannam da Abdullahi Bala da Shafi'u Idris Umar da muhammad Ali. Kamar yadda bayanai suka gabata an
yi shekaru da dama da kafuwar
Daular Borno kafin zuwan ElKanemi.
Sarakunan Borno zamanin daular
Elkanemi kafin Rabeh ya ci Borno da
yaki sun hada da: Shehu Mohammed Al-Amin
Elkanemi 1814- 1846 Shehu Umar Kura Umar (1835 -
1853) Dan Shehu Mohammed
Elkanemi Shehu Abdul Rahman Ibn
Muhammad Elkanemi - 1853 -
1854 Shehu Umar Kura Ibn Muhammad
Elkanemi- 1854 - 1880 Shehu Bukar Zarami Kura Ibn
Umar - 1880 - 1884 Shehu Ibrahim Ibn Umar - 1884 -
1885 Shehu Hashimi Ibn Umar - 1885 -
1893 Shehu Kyari Ibn Bukar Zarami -
1893-1894 Shehu Sanda Limananbe
Wuduroma Ibn Bukar Zarami -
1894 Shehu Umar Kura na cikin Sarakunan
Borno da suka fi dadewa a mulki. Sai Shehu Sanda Kyari wanda ya shafe
shekara kusan 40 yana mulki. Shehu Mustapha Umar El Kanemi shi
ma sarki ne da ya dade inda ya yi
shekara 34 yana mulki. Shehu Garbai kakan Shehu na yanzu
ma ya dade inda ya yi shekara 24
yana mulki. Wanene Rabeh? Tambaya ce da muka samu daga Sani Ali da Nura Bala da ahmad Adam Bagas Minna da Adam Musa Ladan Fulata. Rabeh Zubair Ibn Fadlallah mutum ne
da ya taso daga Sudan, wanda ke
sana'ar fataucin bayi, inda yake saye
ya kuma sayar da bayi. Masanin tarihi Zanna Boguma ya ce
fataucin bayi ne dalilin da ya sa Rabeh
ya yaki Borno . A 1893 ne Rabeh ya kawo wa Borno
hari. "Rabeh Zubair Ibn Fadlallah ne ya
rushe tsohuwar daular Borno bayan
ya kaddamar da yaki kuma ya samu
galabar kwace iko ya mayar da Dikwa
a matsayin babban birnin daularsa". Rabeh ya kashe sarakunan Borno
guda biyu, Shehu Kyarimi da Shehu
Sanda Wudoroma. A 1900 sojojin Faransa na mulkin
mallaka suka kashe Rabeh bayan ya
yi mulki a shekaru bakwai da watanni
bakwai da kwanaki bakwai a Borno. Bayan sun kashe Rabeh ne suka aza
Shehu Sanda Kura daga zuriyar
Elkanemi a matsayin Shehun Borno a
Dikwa a 1900. A 1901 suka tube shi suka kuma
daura dan uwansa Umar Abubakar
Garbai, kakan Shehun Borno na
yanzu. Lokacin Turawan mulkin Mallaka,
tsohuwar Masarautar Borno ta rabu
gida biyu inda Dikwa ta koma
karkashin ikon turawan mulkin
mallaka na Jamus, bisa wata
yarjejeniya tsakanin turawan Faransa da Birtaniya da kuma Jamus na
mulkin mallaka. Daga baya Abubakar Garbai ya koma
Sarkin Borno a yankin da turawan
Birtaniya ke iko. A shekarar 1902 ya fara yin hijira
zuwa Monguno kafin daga baya ya
koma Maiduguri. Lokacin da Dikwa ta koma karkashin
ikon Birtaniya, an samu Shehu guda
biyu, Shehun Borno a Maiduguri da
kuma Shehun Dikwa. Tsarin sarautar Borno. Wannan tambaya ce da muka samu daga Aminudden Ali Dan Hassan. An kafa masarautar Borno da
al'adunta ne a kan tsari na musulunci. Masanin tarihi Zanna Boguma ya ce a
zamanin farko na El Kanemi an bi tsari
ne irin na khalifancin Manzo SAW. Ya ce El Kanemi yana da mashawarta
guda hudu wadanda kuma suka
kasance kamar majalisar Koli. "Mutanen sun hada da Malam
Muhammed Terab da Malam Ahmad
Gonimi da Ibrahim Wadaima da Aji
Sudani wadanda suka taimaka masa
wajen shinfida tsari na shari'a da
adalci a Borno". Amma ya ce bisa tsari na al'ada Borno
tana da tsarin sarautu 3,333,
wadanda suka kunshi na 'ya'yan
gidan sarki da fadawa da bayi da na
Malamai. Sannan akwai sarautu na sana'o'i
kamar na wanzanci da kira da rini. Amma sarautun da suke da girma da
kima sun kai 313. Yadda ake zaben Sarki a Borno - Tambaya ce da muka samu daga Aminudden Ali Dan Hassan Idan Sarki ya rasu, bayan an yi
jana'izarsa za a sanar da hukuma a
rubuce cewa Sarki ya rasu. Daga nan wadanda ke da alhakin
zaben sabon Sarki za su zauna su yi
shawara sannan su fitar da sunaye
daga gidajen saraurar Borno. Idan sun zabi sabon sarki za su mika
wa gwamnati ta sanar. "Masu zaben sabon Sarki guda
bakwai ne da suka hada da Shettima
Kanuribe da Shettima Kuburibe da
Yarima da Kaigama da Mallam Terab"
a cewar Zannah Boguma. Ko Daular Usmaniya ta yaki Daular Borno? Tambaya ce da muka samu daga Abdulmajid Abubakar da Muhammd Yusuf da Umar Abubakar Zamfara da Mudassiru Yusuf S/Fada da Kamal Y Iyantama da Ahmed Rufa'i Abdullahi da Musa Yayan Baba Jihadin Shehu Usman Danfodio ya
faru ne a 1804, inda ya kafa tuta da
daulolinsa a kasashen Hausa a 1805. Danfodio bai yi niyyar ya yaki Borno
ba, amma Fulani da suke zaune a
Borno da ake kira Fulata Borno
karkashin wani babban malami Goni
Mukhtar suka kaddamar da yaki. Malam Goni Muktar ya rubutawa
Danfodio wasika yana son a ba shi
tuta, yana ganin Borno na bukatar a
kaddamar da yaki na jihadi saboda a
ganinsa akwai wasu abubuwan da
ake yi na al'adu. Danfodio ya amince da bukatarsa aka
yaki Borno. "Amma bayan yakin, El Kanemi ya
rubutawa Danfodio da takarda cewa
bai kamata a yaki Borno ba domin
kasa ce ta musulunci da
sarakunanta", a cewar Zanna
Boguma. Ya kara da cewa akwai rubutun
wasikar El Kanemi zuwa ga Danfodio
a cikin litaffin Infakul Maisuri na
Muhammadu Bello Danfodio. "A cikin wasikar El kanemi ya nuna
cewa yakin da aka kaddamar ba
jihadi ba ne illa neman mulki da son
duniya". "Daga baya Danfodio da El Kanemi
sun dawo sun fahimci juna inda suka
amince kuma suka tabbatar da cewa
babu abin da ke tsakaninsu illa aminci
da 'yan uwantaka ta addinin
musulunci". Zanna Boguma ya ce Borno ba ta taba
zama a karkashin tutar daular
Usmaniya ba domin Borno tana da
tarihi na musulunci da malamanta
sama da shekara 1000 kafin kafuwar
daular Usmaniya a Sokoto. "Hakan ya sanya da aka yi bikin cika
shekaru 200 da kafuwar Daular
Usman Danfodio muka ce bai shafe
mu ba, sai mu muka yi bikin shekaru
1000 da kafuwar daular musulunci ta
Borno".
Created at 2018-02-28 10:31:48
Back to posts
UNDER MAINTENANCE