HomeBlogBARKA DA ZUWA DANDALIN DAMAGARWA ZINDER TA JANHURIYAR NIGER. FILINE: NA FADARKAWA NISHADANTARWA DA ILMANTARWA HARDA SADA ZUMUNCI.Zinder garin mune

FALARAR ZIKIRI GA MASU IMANI

FALARAR ZIKIRI GA MASU IMANI
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM Hakika dukkan Malamai Masanan Allah sun tabbatar da cewa babu wani abu guda daya wanda yake bude Zuciyar 'dan Adam fiye da Zikirin Allah. Kuma babu aiki mafi sauki kuma mai kawowa mutum lada masu yawa acikin Qankanin lokaci kamar Zikirin Allah. Kuma babu aiki mafi daraja awajen Allah fiye da Zikiri. Shi yasa ma Madaukakin Sarkin yace : "KU AMBACENI NIMA ZAN AMBACEKU". Kuma yace "KU AMBACI ALLAH, AMBATO MAI YAWA, KUMA KU TSARKAKE SUNANSA (TASBEEHI) SAFIYA DA MARAICE". Kuma babu wata katanga mafi Qarfi wacce take tsare mutum sannan ta kubutar dashi daga Sharri da makircin Shaitan fiye da Zikirin Allah. Hakika shi Zikirin Allah, wata Aljannah ce adoron Qasa wacce duk wanda bai shiga cikinta anan duniya ba, to ba zai shiga waccen Aljannar ta lahira ba. Zikirin Allah shi kadai ne yake ceton zukata daga 'dimuwa da tsoro da firgici, Kuma shine hanya mafi sauki domin samun isuwa zuwa ga kowanne babban rabo da dacewa. Leka cikin Alqur'ani mai girma kaga manyan manyan Fa'idodinsa. Idan kayi nazari za kaga cewa shine babban Sabulun dake wanke ma Zukata dattin Tsoro da bakin ciki da damuwa, Kuma shi ke samar da rayuwa ga zukata. Idan kayi nazari dole kayi mamakin yadda Gafalallu suke rayuwa ba tare da ambatonsa ba. "SU MATATTU NE BA RAYAYYU BA, KUMA BA ZASU SAN YAUSHE NE ZA'A TASHESU BA". Gwargwadon yadda ka nitse cikin ambatonsa, gwargwadon haka hasken zuciyarka yake Qaruwa, tunaninka yake budewa, Dogaronka gareshi yake Qarfafa, to Gwargwadon haka kake qara kyautata zatonka gareshi. Shi Makusanci ne yayin da kayi kiransa, Mai ji ne yayin da ka ambaceshi, kuma mai bayarwa ne yayin da ka rokeshi. Don haka 'dan uwa, Mika bukatarka gareshi, ka Qaskantar da kanka wajensa, Ka maimaita ambaton sunayensa tsarkaka masu dadi akan harshenka. Kana yabonsa da rokon Gafararsa da mika Qokon bararka wajensa. Da sannu zaka samu jin dadi da yayewar bakin cikinka, da aminci, da arziki da nutsuwa, da dacewa da haske. Ga kuma lada marar yankewa. Ya Allah ka sanyamu cikin ALMUFARRIDUN, Masu ambaton Allah da yawa maza da mata. Salati da aminci su tabbata ga Shugaban masu ambaton Allah, cikakken Masoyin Allah, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa da Salihan Bayin Allah baki daya.
Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE
ZINDER GARIN MALAMMAI
Please log in or sign up to chat

Welcome

Hey, zinderniger.wapdale.com - this is a placeholder text on your new XtGem mobile site. To add more content or modify this text snippet use the building tool and start publishing stories, links, pictures using our easy-to-use visual publishing tool. XtGem is a visual mobile site building tool and online presence enabler, allowing users to create and host their very own mobile site. We provide PHP support, no forced ads and lots of other advanced features, such as custom domains or full source code editing support.

ZINDER GARIN MUNE

Duck hunt